Yaron Osama bin Laden na shirin ɗaukan fansan mahaifinsa akan Amurka
- Yaron shahararren dan kungiyar Al-qa'ida Osama bn Laden yayi alwashin daukan fansan mahaifinsa
- Hamza bin Laden ya aika da sakonni zafafa guda hudu zuwa ga kasar Amurka
Rahotanni na nuni da cewar karamin yaron tsohon shugaban kungiyar Al-qa’ida wato Osama bin Laden, mai suna Hamza ya fara shirye shiryen zama sabon shugaban kungiyar, tare da shirin daukan fansan mahaifinsa akan Amurka.
Rahotannin da Legit.ng ta samo sun bayyana cewar an ga wasu wasiku a daren da aka kashe Osama dake cewar Hamza bn Laden ya dau alwashin daukar fansa, kuma ya fara shirya cin ma burin nasa.
KU KARANTA: Sabbin abubuwa 10 da kwamadan Boko Haram ya fada cikin sabon faifan bidiyo
Wani tsohon jami’in hukumar FBI, Ali Soufan yayin dayake ganawa da wata gidan talabijin, CBS yace:
“Hamza ya fadi a cikin wasikar cewar, yana tuna duk irin kallon soyayyar da mahaifinsa ke yi masa, duk murmushin dayake yi masa, da kuma duk kalaman dayake fada masa.”
Soufan yace Hamza na ganin shine magajin Osama. Ko a lokacin dayake karamin yaro, mahaifinsa na amfani da shi a cikin bidiyo, zaka gansa dauke da bindiga. Soufane yace:
“Kalaman da yaron ya fitar a yan kwanakin da suka gabata ya nuna cewa ya fara gadan mahaifinsa, inda ya dinga amfani da daidai kalaman da ubansa ke amfani dasu a fayafayan bidiyo”
Zuwa yanzu, Hamza mai shekaru 28 ya aika ma kasar Amurka sakonnin guda hudu a shekaru 2.
“Yana yawan fadin, jama’an Amurka, zamu zo, kuma zaku ji a jikinku, kuma zamu dauki fansan abinda kukayi ma babana, Iraqi, da Afghanistan, sai mun dau fansa.” Inji Soufan
A wani hannun kuma, jami’an rundunar sojin Najeriya tayi ram da wani kwamandan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a ranar Asabar, kamar yadda Kaakakin rundunar Birgediya Kuka Sheka ya bayyana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli yadda sojoji ke fafatawa da yan Boko Haram
Asali: Legit.ng