An gano gawar 'yar Fira'auna a Masar (Hotuna)
- An gano gawar 'yar Fira'auna a kusa da wata dala mai dumbin tarihi a kasar Masar
- Ma'aikatar kula da kayan tarihi ta ce an gano wani akwatin katako a cikin kabarin
An yi amannar cewa an gano kabarin 'yar Fir'auna a kusa da wata dala mai dumbin tarihi da ita ma aka gano ta a baya-bayan nan a Masar.
Ma'aikatar kula da kayan tarihi ta ce kabarin wanda ke kusa da masarautar Dahshur a Kudancin birnin Al-Kahira, an gano wani akwatin katako a cikinsa.
A cikin akwatin an samu wasu gora guda hudu cike da sassan jikin mamaciyar, wadda aka fi tsammanin cewa 'yar Sarki Emnikamaw ce.
Kamar yadda Legit.ng ke da labara, ginin dalar masarautar sarkin ta kai nisan mita 600 daga kabarin.
KU KARANTA KUMA: Daukar sabbin matakai kan sarkin Kano ba dai-dai bane - Inji Bafarawa
A watan da ya gabata, masu hakar kayan tarihi a karkashin kasa wadanda suke bincike kan burbushin ginin sun gano wani rubutu mai dauke da layi 10 da sunan Emnikamaw.
A masarautar Dahshur ne sarki Sneferu na daula ta hudu ya gina dala mai dumbin tarihi ta farko a Masar, mai tsawon mita 104 da fadin taku 341, kusan shekara 4,600 da ta gabata.
Bayan Sarki Sneferu ya mutu sai dansa Khufu ya gaje shi, wanda ya shahara don gina gawurtacciyar dala a Giza, mai tsawon mita 138, wanda hakan ya zama wani abin mamaki ga duniya a wancan lokaci.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa
Asali: Legit.ng