Hotunan Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu

Hotunan Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu

– Mafi yawan Gwamnonin Arewa su na da ofisihin Uwargida na iyalan su

– Sai dai wasu Gwamnonin ba su jefa matan su cikin harkar shugabanci ba

– Ga dai kadan daga cikin matan Gwamnonin Arewa maso yamma

Legit.ng ta kawo maku hotunan matan Gwamnonin Arewa

Irin su Gwamna Ibrahim Geidam dai ba a san matar sa ba.

Don wasu Gwamnonin ba su bari matan su su shiga cikin sha’anin mulki

KU KARANTA: Ka ji masu shirin tsige Buhari

1. Matar Gwamnan Jihar Adamawa: Hajiya Maryam Muhammad Umar Jibrilla

Hotunan Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu
Uwargidan Gwamnan Adamawa

Matar Gwamnan Jihar Adamawa ‘yar gidan Sani Zangon-Daura ce wanda fitacce ne a Katsina da Najeriya. Tayi karatu har Digir-gir a Kasar Birtaniya.

2. Matar Gwamnan Jihar Bauchi: Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar

Hotunan Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu
Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi

Abin da zai burge ka shi ne tun shekarar 1979 ta auri Mijin ta wanda yanzu ya zama Gwamna. Tayi Digiri har 2 a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

KU KARANTA: Yadda aka ceto 'Yan matan Chibok

3. Matar Gwamnan Jihar Borno: Hajia Nana Kashim Shettima

Hotunan Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu
Uwargidan Gwamnan Jihar Borno

Ana mata lakabi da Uwar Marayu ita ma tayi karatu a Jami’ar Maiduguri kamar dai Mijin ta Kashim Shettima.

4. Matar Gwamnan Jihar Gombe: Hajia Adama Dankwambo

Hotunan Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu
Uwargidar Gwamnan Jihar Gombe

Uwargidar Mai girma Gwamna Dankwambo na Jihar Gombe kuma tana bakin kokari wajen dafawa Mijin ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Buhari zai tsaya takara a zabe mai zuwa ne?

Asali: Legit.ng

Online view pixel