Mai kama da Messi ya shiga hannun 'yan sanda a Iran
- A karshen mako ne, aka samu wani rudani wanda har sai da 'yan sanda suka dauke wani dalibi dan kasar Iran suka kai shi ofishinsu saboda yana matukar kama da Lionel Messi
- Mutane da yawa a birnin Hamaden na kasar ta Iran suna son daukar hoto da dalibin mai suna Reza Parastesh yayin da 'yan sanda suka kama motarsa domin dakatar da rudanin da hakan ya haddasa.
Legit.ng ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne, watanni kadan bayan da mahaifin Reza Parastesh ya sa dan nasa ya dauki hoto da rigar Barcelona mai lamba 10 irin ta Messi.
Daga nan sai matashin mai shekara 25 ya fara yin aski tare da barin gemunsa kamar yadda Messi yake yi.
Ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Yanzu mutane suna daukarsa a matsayin Messi na Iran, kuma suna so in rika kwaikwayon duk abin da yake yi. Idan na je wani wurin sai ka ga mutane suna matukar mamaki.
" Ina matukar murna ganin cewa ganina zai sanya wasu farin ciki, kuma wannan farin ciki yakan sa ni farin ciki sosai."
Ya kuma ce yana koyon yadda ake wasu abubuwan a wasan kwallon kafa ta yadda zai zama kamar Messin sosai.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng