Wata yarinya 'Yar shekara 18 ta yi digiri a karatun lauya da daraja ta 1

Wata yarinya 'Yar shekara 18 ta yi digiri a karatun lauya da daraja ta 1

- Wata matashiya haifaffiyar Najeriya ta zama mafi karantar shekaru da ta kammala karatun aikin lauya a Kwalejin Fourah Bay, ta Jami'ar Saliyo.

- Joy Oluwagbemileke Jegede ta samu sakamako mai daraja ta daya a karatun digiri, tana 'yar shekara 18, shekara daya bayan da ta samu digiri a fannin tafiyar da kasuwanci ta hanyar karatu daga nesa.

Legit.ng ta samu labarin Iyayen Joy wadanda 'yan mishan ne, sun yi kaura zuwa Saliyo lokacin da take da shekara hudu.

Tana da shekara 13 ta rubuta jarrabawarta ta kammala sakandare.

A wata hira da ta yi da wakilin majiyar mu ta BBC, Umaru Fofana a birnin Freetown ta bayyana cewa, "Abu ne da ya fara kamar wasa. Mahaifina na yi wa daliban da zasu rubuta jarabawar kamala karatun sakandire ta WASC bita, a karshen jawabin sai ya tambaye ni, ko za ki so ki rututa da su? Na yarda kuma na fara shiri domin cimma wannan buri."

Wata yarinya 'Yar shekara 18 ta yi digiri a karatun lauya da daraja ta 1
Wata yarinya 'Yar shekara 18 ta yi digiri a karatun lauya da daraja ta 1

KU KARANTA: An shawarci yan PDP da kada su halarci zaman kotun shari'ar Sule Lamido

"A karshen jarabawar, na sami makin A guda uku da makin B guda hudu da kuma maki C daya," in ji Joy.

Ta kara da cewa, "Domin cimma wannan buri iyayena sun taka muhimmiyar rawa. Mahaifiyata ta rika koya mini darasin Lissafi wato Maths yayin da mahaifina ya koya mini darasin Biology. Suka ta yi mini addua'a domin in samu ci gaba a rayuwata."

Misis Joy ta kuma ce, "Yanzu ni ce karama a ajinmu kuma hakan abin alfahari ne."

Ta ce kamata ya yi dalibai su fahimci cewa, fahimtar darasin da ake koya maka ya fi samun sakamako mai kyau.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel