Real Madrid na shirin kafa tarihi a Gasar Champions League
– Kungiyar Real Madrid ta doke makwabtan ta Atletico Madrid a gida
– Real Madrid tayi nasara da ci uku da nema
– Hatsabibin Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kara jefa kwallaye 3
Wannan karo ma dai kuma babban Dan wasa Ronaldo ya kara zura kwallaye 3 a Gasar UEFA Champions league.
Real Madrid ta doke Kungiyar Atletico Madrid 3-0 a zagaye na farko na wasan na-kusa da karshe.
Monaco za ta fafata Kungiyar Juventus.
Zakarun UEFA Champions league Kungiyar Real Madrid na iya kafa tarihi idan su ka kara daga kofin a bana. Babu wanda ya taba daukar kofin dai sau biyu a jere tun da aka sauya Gasar na zakarun Turai.
KU KARANTA: Idan El-Rufai na Real-Madrid, ina Barcelona-Shehu Sani
Dan wasa Ronaldo dai ya kafa tarihi inda ya zama Dan wasan da ya jefa kwallaye 3 a wasanni biyu a jere a Gasar. Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ne ya jefa kwallaye 3 duk shi kadai a wasan su da Bayern Munich haka kuma ya kara yi a wasan jiya.
Ana fara wasan Ronaldo ya jefa kwallo guda a raga. Bayan wasan yayi nisa kuma ya kara daya, kafin dai a tashi su ka zama uku. Real Madrid da musamman Ronaldo sun raina Kungiyar Atletico inda ya zura masu kwallaye kusan 20 a ragar su shi kadai.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wani Babban Mawakin Najeriya Iyanya
Asali: Legit.ng