Hotunan shagulgulan auren mawaki Nura M. Inuwa
-Anyi bikin auren mawakin Kannywood Nura M Inuwa a jihar Katsina
-Manyan jaruman Kannywood maza da mata sun halarci bikin
Daga karshe dai anyi bikin auren shahararren mawakin Kannywood Nura M Inuwa da Amaryarsa, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
A ranar Alhamis 27 ga watan Afrilu ne aka fara gudanar da shagulgulan bikin a jihar Katsina inda aka farad a wasan kwallon kafa da kamu a ranar Alhamis.
KU KARANTA: Matsafa sun aika da wata kurciya mai dauke da asiri jihar Kano
Yayin da Dinner ya biyo baya a ranar Juma’a 28 ga watan Afrilu, sannan aka daura aure a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu a garin Malumfashi.
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar bikin ya samu halartar manya manyan mawakan Hausa da jaruman Kannywood da dama.
Ga wasu daga cikin Hotunan auren:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Jama'a menene ra'ayinku?
Asali: Legit.ng