Dandalin Kannywood: Ummi Zee Zee ta zama tsohon yayi yanzu - Umma Shehu

Dandalin Kannywood: Ummi Zee Zee ta zama tsohon yayi yanzu - Umma Shehu

- Shahararriyar ‘Yar wasan fina-finan Hausa Umma Shehu ta mai wa Ummi ZeeZee martini kan cewa da tayi wai har yanzu ta fi duk wata ‘yar wasan Hausa Aji.

- Ta ce ZeeZee ba ta isa ta hada kanta da jaruman da suke fim ba yanzu.

- Ta kara da cewa ko ada din ma ZeeZee ba wata aba bace a harkar fim domin bata kai matsayin jarumai irin su Fati Mohammed ba, Safiya Musa da su Mansurah Isah ba.

Ta ce Jarumai kamarsu Jameela Nagudu, Nafeesat Abdullahi, Aisha Tsamiya, Hadiza gabon sun yi mata zarra kuma ko yanzu ta dawo babu wata rawar da zata iya takawa da zai zarce su da suke farfajiyar a yanzu.

Jaruma Umma Shehu ta bayya hakan ne a cikin wata fira da tayi da gidan jaridar Premium Times Hausa.

Legit.ng ta ambato cewa da jaridar ta tambayeta ko menene zata ce akan furicin da ZeeZee ta yi wai tafi ku aji har yanzu?

Dandalin Kannywood: Ummi Zee Zee ta zama tsohon yayi yanzu - Umma Shehu
Dandalin Kannywood: Ummi Zee Zee ta zama tsohon yayi yanzu - Umma Shehu
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashin Lafiyar Buhari: Kuskure ne mu tsaya a sake maimaita Yar'adua

Sai Umma ta kada baki tace: "Wannan ra’ayin tane amma ni na sani cewa ko a zamanin da take fim, it aba sa’an su Fati Mohammed, ko Safiya Musa da dai sauransu bane. Ta dai yi iya abin da zata iya ballan tana yanzu da akwai gwanaye da yawa.

Tana dai neman a waiwaye ta ne kawai amma ba wai hakan bane. Amma jaruman yanzu ai ba sa’o’in ta bane. Ko dawowa tayi yanzu babu tasirin da zatayi a harkar fim domin an riga an wuce sanin ta."

Da kuma aka kara tambayar ta ko bata ganin ko don tana ganin baku kware bane har yanzu ko kuma ba kwa birgeta?

Sa ta sake bude baki tace: "ZeeZee dai ta fadi abinda ta ke so ta fadi amma kowa yasan ba haka bane. Kamar yadda na gaya maka. An riga anyi mata zarra yanzu kuma ko ta dawo sai dai tayi kallo amma bawai ta yi wani abinda jaruman yanzu ba sayi ba."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel