Tattali: Naira ta sha kasa kadan a jiya
– Darajar Naira ta dan yi kasa kadan kuma a jiya Alhamis
– Naira ta sha kasa a kan Dalar Amurka
– Sai dai ba ta motsa kan sauran kudin kasar waje ba
Legit.ng na da labarin cewa Dala ta dan girgiza kadan a kasuwar canji.
Dalar ta dan fadi kadan kan Dalar Amurka.
Sai dai ba ta sha kasa a kan wasu kudin kasar waje ba.
An dai saida Naira a bankuna kan N305 a jiya. Hakan dai na nuna cewa Dalar ta dan daga kadan a kan Naira. Pounds Sterling da kuma Dalar EURO suna nan su motsa ba. An kuma saida Dala a kasuwa a kan N390 kenan an samu karin kusan N2 daga yadda aka saida a Shekaran jiya.
KU KARANTA: Naira ta daga sama a kasuwa
Dalar dai tana da farashi dabam-dabam. Akwai na kasuwa, da na banki, akwai kuma na mahajjata, akwai na CBN da kuma farashin BDC na yan canji wanda duk mabanbanta ne. Dalar dai ta tashi ne daga N520 zuwa kusan N380
Babban bankin kasar nan watau CBN ya bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga cikin matsin da ta shiga na durkushewar tattalin arziki. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya bayyana wannan ne bayan ya ganan da Majalisar Dattawa.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ya za ayi da barayi?
Asali: Legit.ng