Kundin Kannywood: Tauraruwar Halima Atete ta haska sosai (Hotuna)

Kundin Kannywood: Tauraruwar Halima Atete ta haska sosai (Hotuna)

- Jaruma Halima Atete ta daka masoyan Nafisa Abdullahi wawa, domin ta sami karin masoya doriya akan wanda take dasu abaya.

- Tun lokacin da Halima Atete taki yarda ta aske gashin kanta sai mutane suka kara sonta, ta hanyar jinjinawa jarumar akan wannan namijin kokari da tayi.

Wannan abin ya janyowa Halima Atete farin jini a idanun duniya. Akwai mutane da yawa wanda suke yiwa Halima kallon hadarin kaji abaya, amma yanzu sun daina sabida sun yaba hankalin Halima Atete.

Legit.ng sun tattaro masu magana da yawun Halima Atete Mustapha 142 Maidiguri yace tabbas Halima tayi kyan kai. Kuma dama yasan duk abinda take yi kafin tayi sai tayi nazari. Akwai fina finai masu tarin yawa wanda idan anba Halima ta fito amatsayin jaruma to ba zata yi ba. Sabida Halima macace mai tarbiya da alkunya gamida hakuri.

Kundin Kannywood: Tauraruwar Halima Atete ta haska sosai (Hotuna)
Kundin Kannywood: Tauraruwar Halima Atete ta haska sosai (Hotuna)

KU KARANTA: Buhari ma ya maidawa Jonathan martani

Duk masifar da akaga tana yi a fim to azahiri ba haka take ba. Halima Atete ba masifaffiya bace afili macace mai hakuri da barkwanci gamida karrama masoyanta. Abaya ni masoyintana kawai, amma da ta gane irin kaunar da nake yi mata sai ta janyo ni jikin ta. Ina jin abinci a karkashin ta. Inji Mustapha.

To, a nawa ra'ayi dukkansu Nafisa da Halima sun canci yabo gamida jinjina. Ita Nafisa za'a jinjina matane sabida ta ruke sana'arta da gaskiya. Domin ta nuna ko maye zata yi akan sana' arka. Dama hausawa sunce "sana'arka abar alfaharin ka".

Itama Halima tayi kyan kai sabida ta nuna kishin muslimci wanda ya zame mana madubi wajen aikata ko wanne irin abu. Domin samin dacewa duniya da lahira.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel