Duk wanda ya iya taka rawar fim din Rariya zai samu kyauta mai girma daga Rahama Sadau

Duk wanda ya iya taka rawar fim din Rariya zai samu kyauta mai girma daga Rahama Sadau

- Akwai wata rawa ta musamman da Rahama tayi da jarumi Ali Nuhu a fim din Rariya inda ta sanarwa masoyanta da duk wani mai kaunarta kai har da wanda ba haka ba da a je ayi wannan rawa da irin basirar mutum sanna a saka a shafinta na Instagram ko Facebook

- Ta sha alwashin ba duk wanda ya iya rawan kyauta mai tsoka

Rahama Sadau dai ba boyayyiya bace a farfajiyar fina-finan Hausa. Bayan shahara da tayi a iya rawa da rangwada ta na birgewa a duk fannin da aka dora a fim.

Rahama cikin lokaci dan kadan ta zarce da yawa daga cikin wadanda ta riska a farfajiyar fina-finai din.

A daidai tauraruwarta na shanawa ne kwatsam ta tafka laifin da masu kula da yadda ake gudanar da al’amurar shirya-fina fina-finan Hausa suka kore a farfajiyar.

Duk wanda ya iya taka rawar fim din Rariya zai samu kyauta mai girma daga Rahama Sadau
Rahama Sadau da Ali Nuhu

Wannan kora dai ya sa Rahama ta sami daukakar da bata taba tsammani ba a rayuwar ta.

KU KARANTA KUMA: Uwargidan Najeriya tayi wani gagarumin kokari

Ko da yake ance kowa ya bar gida, gida ta barshi, ga dukkan alamu dai Rahama na kwadayin ta dawo farfajiyar fina-finan Hausa.

Gab da za’a kore ta ta shirya fim din ta na farko mai suna RARIYA wanda manyan jarumai a fim din Hausa suka fito a ciki.

To, fim din dai yana gab da ya fito domin an dan tsokata wa masu kallo wasu daga cikin fim din.

Akwai wata rawa ta musamman da tayi da jarumi Ali Nuhu a fim din inda ta sanarwa masoyanta da duk wani mai kaunarta kai har da wanda ba haka ba da a je ayi wannan rawa da irin basirar mutum sanna a saka a shafinta na Instagram ko Facebook.

Wanda duk tashi tayi zarra zai samu kyauta ta musammam daga Rahama Sadau.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar yan fensho na kasa sun karrama Gwamnoni 6

Daruruwan mutane sun amsa wannan kira inda har yanzu ana ta aikawa da bidiyon rawan

wanda mutane sukayi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wata mata mai sana'ar maza a Jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel