Matsaloli 7 da shan gishiri da yawa ke haifar wa dan Adam (Karanta)
- Gishirin da ake amfani da shi wajen kara dandanon girki na dauke da sinadarin ‘sodium’ wanda ke da matukar amfani a jiki idan ba a ci shi fiye da kima ba.
- A yayin da sinadarin ya wuce yadda ake bukatar shi a jikin dan adam, a lokacin ne mutum zai fara fuskantar matsaloli ga lafiyar sa iri iri kamar su hawan jini da ciwon zuciya.
Adadin gishiri da ya kamata mutum ya ci a kullum, wanda kuma ba a son ya wuce haka shi ne miligram 2300, kimanin cikin cokalin shan shayi kenan.
Sai dai kash da yawa a cikin mu na cin fiye da haka ba tare da mun sani ba, musamman ma idan mutum ya na da ciye ciye.
Legit.ng ta tattaro maku kadan daga cikin alamomin da ka iya nunawa mutum cewa yana cin gishiri fiye da kima:
1. Toshewar kwakwalwa, ta yadda mutum zai ji kamar an zuba masa dussa a ciki. Tuna abubuwa ko yin abubuwan da ke bukatar amfani da kwakwalwa ya kan yi wahala.
2. Abinci ba ya yi wa mutum dandano a baki. Idan har ka samu kanka ka na neman gishiri domin ka kara a abinci, kuma sauran mutane ba su nemi kari ba, wannan alama ce da ke nuna cin gishiri da yawa.
KU KARANTA: Kiristoci na taya yan shi'a jimami
3. Yawan jin kishi ruwa: idan mutum ya kasance ko da yaushe bakin sa a bushe yake, ya na bukatar ruwa, wannan ka iya kasancewa a sakamakon gishiri da ya yi yawa a koda, wacce take bukatar ruwa domin ta wanke shi.
4. Kumburin jiki: Idan ka samu kwatsam jikin ka ya kumbura, musamman ma ciki, toh wannan alama ce da ke nuna cewa gishirin da ke cikin jini ya wuce kima.
5. Gyambon ciki (Ulcer): Gishiri da yawa a cikin ciki ka iya cinye fatar ciki ya haifar da gyambo. Ga masu gyambon ciki, ya na da kyau mutum ya duba adadin gishirin da yake ci a kullum ko shi ke haifar masa da matsala.
6. Hawan jini: Inda mutum ya je asibiti aka ce masa jinin sa ya hau, akwai yiyuwar cin gishiri da yawa ne ya haifar da haka.
7. Ciwon koda: Yawan sinadarin sodium a jiki ya na hana koda ta yi aiki yadda ya kamata. Idan mutum yana cin gishiri fiye da kima kuma yaje asibiti aka ce masa ya na da ciwon koda, toh tabbas wannan gishiri shi ne sila.
Da fatan za mu kiyaye.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyon anfanin kokonba
Asali: Legit.ng