Abubuwa da Hukumar Alhazai ta Najeriya ta shirya wa alhazai da za su amfana a wannan shekara ta aikin hajji
- Ba za a fitar da kudin aikin hajji na bai-daya a tsakanin jihohin kasar ba
- Za a sanar da kudin hajji ne dai-dai da hidimar da kowace jihar
- Kawo yanzu ba a tsayar da kudin kujerar aikin hajjin bana ba
- Alhazai za su samu mahalli mai inganci kuma kusa da harami
Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce a bana ba za a fitar da kudin aikin hajji na bai-daya a tsakanin jihohin kasar ba.
KU KARANTA: Malaman Izala sun kai ma Sarki Muhammadu Sunusi II ziyara (Hotuna)
Shugaban hukumar, Abdullahi Mukhtar Muhammad, ya ce za a sanar da kudin hajji ne dai-dai da hidimar da kowace jihar za ta yi wa alhajinta.
Legit.ng ya ruwaito cewa, Abdullahi Mukhtar ya kuma ce kawo yanzu ba a tsayar da kudin kujerar aikin hajjin bana ba.
KU KARANTA: Kamannin shugaba Buhari ya yi bikin murnar ranar haihuwarsa a Abuja
Dangane da jin dadin alhazai, Mukhtar ya ce alhazai za su samu mahalli mai inganci kuma kusa da harami kamar yadda sauran kasashen duniya ke samu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wannan Legit.ng bidiyo na nuna direban wani babban fasto na da ya musulunta
Asali: Legit.ng