Sarkin Kano ya karɓi bakoncin kungiyar JIBWIS ta ƙasa a fadarsa
- Shuwagabannin kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah, JIBWIS, ta kasa a karkashin jagorancin shugaban kungiyar Sheikh Bala lau sun kai ma mai martaba Sarkin Kano ziyarar ban girma.
- Wakiliyar jaridar Rariya Sa'adatu Baba Ahmed ta ruwaito Sheikh Bala Lau tare da manyan malaman Izala sun kai ziyarar ne a ranar Litinin 24 ga watan Afrilu inda suka gana da mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a fadarsa dake Kano.
KU KARANTA: Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo
A wani labarin kuma, a ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu ne masarautar Kano ta musanta zargin cewa sarki, Muhammadu Sanusi II, ya kashe naira biliyan 6 na asusun masarautar tunda ya hau karagar mulki.
A wani taron manema labarai a Kano, Walin Kano Bashir Wali, ya fada cewa naira biliyan 2 kacal masarautar ta kashe un da Mallam Sanusi ya hau kujerar sarauta a watan Yuli 2014.
Idan ba’a manta Kwanan Legit.ng ta fara samun jita-jitar cewa wasu Gwamnonin Arewa na kokarin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II inda har aka ce wasu daga cikin Gwamnonin sun yi wani taro game da Sarkin a kasar China.
A kwanan baya ne dai wani Marubuci kuma Dan Jarida mai suna Ja’afar Ja’afar yayi wani rubutu har kashi biyu inda ya bayyana irin makudan kudin da fadar Kano ta rika batarwa wajen sayen manyan motoci da kuma kudi na hawa shafin yanar gizo.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Tsohon soja yayi kira da inyamurai su guji neman Biafara
Asali: Legit.ng