Abu mai karya zuciya: kalli jarumin soja da yan Boko Haram suka kashe
- Yan ta'addan Boko Haram sun kashe wani jami'in soja
- An kashe shi ne a wani harin bazata da yan ta'addan suka kai ma sojoji a jihar Borno
Hoton wani jarumin sojan Najeriya wanda aka kashe a filin daga na ta yawo a yanar gizo.
A cewar Auwal Shuaib Jikan Mesa, wani mai amfani da shafin Facebook ya buga hoton, sojan mai suna Abubakar Hassan ya rasa ransa a wani harin bazata da yan ta’addan Boko Haram suka kai a jihar Borno.
Legit.ng ta tattaro cewa yan ta’addan sun kai ma sojojin harin bazata a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu.
A nan kasa ya kasance hoton jarumin sojan ne wanda abokansa da yan’uwansa bazasu iya daina kukan rashin sa ba.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo
Hukumar sojin Najeriya ta bude magudana mai inganci na dukiyarta domin tabbatar da kawo karshen yan Boko Haram cikin sauri.
Dakarun sojin Najeriya da yan farin hula da dama sun rasa rayukansu a cikin wannan yaki kuma da alama yakin zai kawo karshe ta hanyar zama nasara ga kasar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kaga abinda rikicin kabilanci ke janyowa.
Asali: Legit.ng