Yadda aka yi tsakanin ‘Dan bautar kasa da wani Gwamna

Yadda aka yi tsakanin ‘Dan bautar kasa da wani Gwamna

– Gwamna Ayo Fayose ya ba wani Dan bautar kasa aiki nan take

– Bawan Allah ya bayyanawa Gwamna Fayose cewa yana burge sa

– Ba ayi wata-wata ba Gwamnan yace a ba sa aiki a Jihar

Yadda aka yi tsakanin ‘Dan bautar kasa da wani Gwamna
‘Dan bautar kasa ya samu aiki hannun Gwamna

Legit.ng na da labarin wani Bawan Allah mai bautar kasa watau NYSC a Jihar Ekiti da ya samu aiki a sama bayan ya gana da Gwamnan Jihar Mr. Ayodele Fayose. Dan bautar kasa ya fadawa Gwamna Fayose cewa shi gwanin sa ne.

Yayin da Gwamna Fayose ya kammala wata ziyara da ya kai sai wannan dan bautan kasa mai suna Osamwonyi Bright ya nemi su dauki hoto tare da Gwamnan inda ya bayyana masa saboda shi ya dawo Jihar Ekiti domin irin burge sa da yake yi.

KU KARANTA: Budurwa ta maka wani Fasto a kotu

Yadda aka yi tsakanin ‘Dan bautar kasa da wani Gwamna
‘Dan bautar kasa yayi kasa bayan Gwamna ya ba shi aiki

Mr. Bright ya samu shiga inda yayi hoto tare da Gwamnan ya kuma bayyana masa cewa ya kammala Jami’ar UNIBEN ta Jihar Edo da mataki na farko a fannin harkar siyasa. Ba ayi wata-wata ba Gwamnan ya nemi a ba sa aiki a Kwalejin ilmi na Ikere da ke Jihar Ekiti.

Haka kuma Tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi ya kai karar Gwamna Ayo Fayose Kotu inda yace sun masa sharri su na kuma nema su bata masa suna bayan da su ka ce shi ya mallaki gidan da EFCC ta gano wasu makudan kudi kwanaki a Legas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamna Fayose ya zama dan kida da rawa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel