Zance ya lalace: Budurwa ta kai karar Fasto

Zance ya lalace: Budurwa ta kai karar Fasto

– Kwanaki wani Fasto Johnson Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Makiyaya Fulani

– Sai dai yanzu wannan Faston ya shiga tsaka-mai-wuya

– Wata Budurwa ta maka shi a kotu a kasar waje

Zance ya lalace: Budurwa ta kai karar Fasto
Fasto Sulaiman da iyalin sa

Kwanaki idan ba a manta Legit.ng ta kawo labarin babban Limamin cocin nan na Omega Fire, Fasto Johnson Sulaiman inda yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Fulani a duk inda suka ci karo da su kusa da cocin sa.

Yanzu haka dai wata Budurwa ta maka wanna Fasto a kotu inda ta ke zargin sa da laifin lalata da fyade da karfin tsiya tare da saba alkawari da kuma bata-suna. Stephane Otobo ta kai karar Faston ne a wani kotu a kasar Canada.

KU KARANTA: Ba za mu saki Zakzaky ba Inji Osinbajo

Zance ya lalace: Budurwa ta kai karar Fasto
Budurwa ta kai Fasto Sulaiman

Budurwar tana zargin Faston da kwanciya da ita a Najeriya bayan ya gayyace ta cocin sa. Fasto Sulaiman dai yayi alkawarin zai aure wannan Budurwa kamar yadda ta fada, sai dai yanzu yayi watsi da ita.

Stephane Otobo ta tattara ta baro kasar Canada ta dawo Najeriya domin ta tare da Faston wanda ta ke tunani zai aure ta. Yanzu haka dai za a bukaci Faston ya hallara a gaban Kotu domin shari’a.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamna ya zama Mawaki a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng