Cututtuka 7 da abarba ke magani
– Kayan marmari su na da matukar amfani ga jikin Dan Adam
– Daga cikin masu irin wannan amfani akwai Abarba
– Abarbara na gina jiki kuma yana maganin cututtuka da dama
1. Cutar Ataraitis
Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai damun gabbai da jijiyoyi inda su ke kumbura har su hana mutum sakat. Yawan shan abarbara na maganin wannan ciwo.
2. Cancer
Abarba na maganin cutar ‘kansa’ mai lahanta kwayoyin garkuwa saboda sinadarin da ya kunsa na bitamin A da C da sauran su
3. Sanyi da mura
Ina mai fama da tari da mura? Ya yawaita shan abarba domin kuwa yana kunshe da wasu sinadarai da ke kashe majina.
KU KARANTA: Mahaifiyar Dan wasa ta koma saida burodi
4. Karfin hakori
Kadan daga aikin Abarba akwai kara karfin jijiyoyin hakori har da ma kuma gyara suma watau gashi na jikin mutum.
5. Kaifin gani
Haka kuma abarba na kara kaifin idanu don haka mai shan abarba zai dade da idanun sa garau ko ya tsufa.
6. Hawan jini
Abarba na kare cutar hawan jini saboda sindarin ‘Pottasium’ da take dauke da shi mai amfani wajen yawo da jini a jikin mutum.
7. Abarba na hana tsufa
Ba gyara idanu kurum ko da an tsufa ba, abarba na kare mutum daga irin cutar dimuwa da sauran cututtuka na tsufa
An tsinakayo wannan daga shafin www.organicfacts.net
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ana nema a rusa gidan wata tsohuwa
Asali: Legit.ng