Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah yayiwa Alh Ahmadu Chanchangi rasuwa
Wannan hamshakin maikudi haihuwa jihar Taraba, mazaunin jihar Kaduna, Alh Ahmadu Chanchangi ya rasu ne a hanyar Kaduna zuwa Abuja yayinda ake kokarin kaisa Abuja asibiti da safiyar yau Laraba.
Wata majiya ta bayyana cewa : “Ya rasune a hanya yayinda muke kokarin kaishi asibiti a Abuja, bayan wata rashin lafiya da yayi.”
Ya rasu ya bayar mata 3 da yara 33, daya daga cikinsu shine shugaban kwamitin kwasta na majalisan wakilan tarayya, Rufai Chanchangi.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta bada izinin mayar da masallacin Idi Kasuwa
“Za’ayi jana’izara misalin karfe 1 na rana a gidansa da ke kwanan Chanchancgi Tudun wada Kaduna s kuma za’a kaishi makabartan Bashama Road.”
Daga cikin wadanda suka fara kai ta’ziyya shine mataimakin shugaban masu rinjayen majalisan dattawa, Bala Ibn NA Allah.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng