Sarkin musulamai yayi aman wuta, yace bara bai da tushe a Musulunci

Sarkin musulamai yayi aman wuta, yace bara bai da tushe a Musulunci

- Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa’ad Abubakar ya kaddamar da cewa yin bara a unguwanni baida tushe a Musulunci

- Basaraken ya daura lafin bara a titi a kan lalaci

- Ya bukaci mabarata a titi da su nemi hanyar dogaro da kai na halal

A ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewa bara bashi da asali a cikin addinin Musulunci sannan kuma ya kalubalanci wadanda suka dauki a kan sana’a da su nemi hanyar samun na kai ta hanyar halal.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Abubakar ya bayyana hakan ne a Sakkwato gurin yaye mata 2000 da matar gwamnan jihar Sakkwato Hajiya Mairo Tambuwal ta horar a fannin sana’oi daban daban.

Legit.ng ta tattaro cewa an gudanar da horan ne tare da hadin gwiwar hukumar Zakkah na jihar Sakkwato da hukumar dake horar da mata daga mazabun jihar guda 86.

Sarkin musulamai yayi aman wuta, yace bara bai da tushe a Musulunci
Sarkin musulamai, Alhaji Sa'ad Abubakar

Ya yaba ma uwargidan Tambuwal da ta kirkiri shiri sannan ya shawarci wadanda suka amfana da suyi amfani da damar sosai gurin inganta rayuwar su.

Da farko, matar gwamnan ta nuna godiyar ta ga majalisar Sultan, gwamnatin jihar da kuma hukumar Zakkah kan goyon bayan shirin.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya rasu

Ta kuma bayyana cewa ana gudanar da horon ne domin mata su dogara da kansu a jihar.

Uwargidan Tambuwal, wacce Hajiya Hauwa Muhammad ta wakilce ta, tayi kira ga wadanda suka amfana da suyi aiki da sabon aikin da suka koya gurin daukaka tattalin arzikin su da kuma bayar da gudunmuwa gurin ci gaban jihar.

Shugaban hukumar ta Zakkah, Malam Lawal Maidoki, ya bayyana cewa an zabi mata 2000 sannan kuma aka basu tallafi domin su fice daga sahun talauci.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

A cikin wannan bidiyo na Legit.ng, Sarki Lamido Sanusi ya soki shugabancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: