Taurarin Kannywood sun jaddada mubaya’arsu ga gwamna Ganduje

Taurarin Kannywood sun jaddada mubaya’arsu ga gwamna Ganduje

- Jaruman Kannywood sun tabbatar da goyon bayansu ga gwamnan jihar Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta karbi bakoncin mashirya fina finan Kannywood

Kungiyar 'yan fim magoya bayan gwamnatin jihar Kano mai suna 'Kannywood Movement For Buhari And Ganduje sun kai ziyara fadar gwamnatin Kano a safiyar ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu domin kara karfafa dankon zumunci tsakanin gwamnantin shugaban kasa Buhari da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje masana'antar finafinan Hausa.

Dayake jawabi, kakakin kungiyar, mawaki Sa'eed Nagudu ya kara da cewa, "muna so mu tabbatar wa da gwamnatin jihar Kano cewq muna godiya da abubuwan alkairi da take yi wa masana’antar finafinan Hausa. Sannan kuma muna so mu kara tabbatar wa da gwamnati da al'umma cewa akwai alaka da fahimtar juna mai kyau tsakanin Kannywood da gwamnatin jihar Kano.

KU KARANTA: Yadda ta kasance yayin da shugaban JAMB ya kai ma Buratai ziyara

"Wannan shine dalilin ziyarar mu zuwa gidan Gwamnantin Kano duba da yadda muke bada gudunmawarmu a harkar siyasa a jahar Kano da ma kasa baki daya. Mun sami ganawa da mai baiwa gwamnan shawara, Honarabul Aliyu Yusuf Tumfafi." Kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Taurarin Kannywood sun jaddada mubaya’arsu ga gwamna Ganduje
Nura Hussein

Shima a nasa jawabin, Jagoran tawagar 'yan fim din, Nura Hussein ya bayyana cewa a tarihin Kano ba a taba yin gwamnatin da ta yi 'yam fim halarci ba kamar Ganduje, domin ya baiwa wasu abokan aikin su irin su, Rashida Adamu (Mai Sa'a), Yahanasu Sani, Isma'il Na'Abba Afakallah da sauransu mukamai.

Taurarin Kannywood sun jaddada mubaya’arsu ga gwamna Ganduje
Sani SK

Nura Hussein ya kara da cewa a don haka za su baiwa gwamnatin Buhari da ta Ganduje goyon baya dari bisa dari domin cimma kudirorinsu na ciyar da kasa gaba, musamman na kare dukiyar al'umma.

Taurarin Kannywood sun jaddada mubaya’arsu ga gwamna Ganduje
Jaruman Kannywood

Majiyar Legit.ng ta zayyano sunayen wasu yan Fim da suka halarci taron, kamar su Nura Husaini, Ali Gumzak, Naziru Dan Hajiya, Sa'eed Nagudu, Saleem Ahmed Saleem, Ibrahim Kast, Tahir Lawan, Garzali Miko, Shamsu Dan Iya, Bello Muhammad Bello, Mustapha Musty, Hafiz Ado Baba, Yakubu Husain Barrister, Tijjani Saraki, Kabir Muhammad, Ibrahim L. Ibrahim, Iliya Kefass da Abubakar Sabo Usman.

Taurarin Kannywood sun jaddada mubaya’arsu ga gwamna Ganduje
Taurarin Kannywood

Sauran sun hada da Falalu Dorayi, Sadiq Sani Sadiq, Jazuli Kazaza, Tijjani Asase, Ahmad lamido Bazuka, Hadizan Saima, Hajiya A'isha Ibrahim, Farida Muhd Buhari, Shamsu Dogo, Ahmed Lamido (Amaduwalle), Abbas Muhammad, Babangida (Mr Bangis), Kalil Ibrahim, Abdulrahman Ibrahim da sauransu da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda direban wani fasto ya musulunta

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng