Amfanin tafarnuwa wajen inganta kiwon lafiya guda 9

Amfanin tafarnuwa wajen inganta kiwon lafiya guda 9

- Bincike ta nuna cewa cin tafarnuwa na da matukar amfani a wajen inganta kiwon lafiyar dan Adam.

- Cin tafarnuwa na taimakawa ma'aurata wajen guzuri da Jin dadin jima'i

Akasari ana amfani da tafarnuwa ne wajen kara dandanon girki amma bincike ya tabbatar da cewa ana amfanin da shi wajen rigakafin cututtaka daban daban.

Legit.ng ta kawo wasu daga cikin amfanin tafarnuwa kamar haka:

1. Cutar asma

Tafarnuwa na da tasiri wajen rigakafin cutar asma inda ake bukatar mai cutar a duk dare kafin ya kwanta barci, ya dafa tafarnuwa ya sha da madara.

Amfanin tafarnuwa wajen inganta kiwon lafiya guda 9
Hoton tafarnuwa

Haka ma, wanda cutar ta taso masa, za a iya bashi nikakken tafarnuwa.

2. Tari da sanyi

Ana amfani da tafarnuwa wajen rigakafin sanyi da tari inda ake bukatar mai fama da tari, ya ci garlic din kai tsaye ba tare da hada shi da komai ba.

3. Atini da gudawa

Bincike ya tabbatar da cewa tafarnuwa na kashe kwayoyin cuta da ke cikin ciki wadanda akasari su ke janyo atini da gudawa.

4. Matsalar ido

tafarnuwa ya kunshi sinidarai irinsu, quercetin, selenium da vitamin C wadanda duk suna taimakawa wajen rigakafin cututtukan da suka jibinci ido da kumburinsa.

5. Hawan jini

tafarnuwa na da matukar tasiri wajen Rigakafin cutar hawan jini inda aka lakanci amfani da shi akai akai.

6. Rage kiba

tafarnuwa ya kunshi sinadarin ' allicin' wanda ke kona kitsen da ke da illa a jiki.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Kwastam tayi ram da buhuhunan shinkafa 317

7. Narkewar abinci

Yawan cin tafarnuwa a cikin abinci yana taimaka wajen saurin narkewar abinci a cikin ciki ta yadda sinadiran gina jiki za su shiga cikin jini a kan lokaci.

8. Hawan Jini

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa man da aka tatse daga tafarnuwa na taimakawa mai cutar hawan jini daga kamuwa daga cututtukan da hawan jinin kan haifar.

9. Kara karfin gaban namiji

Sakamakon wani bincike ya nuna tafarnuwa ya kunshi sinadarin ' Aphrodite' wanda ke taimakawa ma'aurata wajen guzuri da Jin dadin jima'i.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku koya yadda za a shirya miyan naman bunsuru a cikin wannan bidiyon

Asali: Legit.ng

Online view pixel