Babban dan wasan Barcelona ba zai samu buga gwabzawar su da Madrid ba
– Babban dan wasan Barcelona Neymar ba zai samu buga wasan su da Real Madrid ba
– Za a buga babban wasan El-Clasico a Ranar Asabar
– Neymar ya samu jan kati a wasan da ya buga da Malaga
Legit.ng na da labari cewa babban dan wasan Barcelona watau Neymar Jr. ba zai samu buga wasan kungiyar da Real Madrid ba wanda za za gwabza a Ranar Asabar. Wannan dai babban rashi ne ga Barcelona.
A wasan da Kungiyar ta buga da Malaga wancan makon, Dan wasa Neymar ya samu jan kati, bugu-da-kari kuma yayi wa Alkalin wasa rashin kunya. Hakan ta sa hukuma ta kara yawan wasannin da ba zai buga ba zuwa 3.
KU KARANTA: Barcelona ta sha kashi hannun Juventus
Malaga dai ta doke Barcelona a wasan da ci 2-0 wanda hakan ya hana ta kara matsayi a teburin La-liga bayan Real Madrid tayi kunnen-doki da makwabtan ta watau Kungiyar Atletico Madrid ta rana. Watakila a rage hukuncin amma dai Madrid ita ma za ta take babu dan wasa Pepe a baya.
Har wa yau dai Kungiyar Juventus ta ba Barcelona dan-karen kashi a gasar UEFA Champions league na zakarun turai. Juventus ta biyo Barcelona har gida kasar Spain ta zuba mata kwallaye 3 a raga.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
'Yan kwallon Super-Eagles na Najeriya
Asali: Legit.ng