Wani Dan wasa ya kammala karatun Digirgir

Wani Dan wasa ya kammala karatun Digirgir

– Babban Dan wasan kwallo Girogio Chiellini ya kammala karatu a Jami’a

– Dan wasa Chiellini yayi karatun Digirgir a Jami’ar Turin

– Chiellini rikakken Dan wasan baya ne a Kungiyar Juventus

Wani Dan wasa ya kammala karatun Digirgir
Ashe ba taka leda kurum Dan wasan ya iya ba

Legit.ng ta samun labarin cewa shahararren dan wasan kwallon kafar nan mai suna Girogio Chiellini ya kammala karatun sa a Jami’a. Wannan dai ya nuna cewa ashe cin danko ba sai kaza kurum ba.

Babban dan wasan bayan ya kammala karatun Digirin sa na biyu a fannin harkar kasuwanci watau M. BA. Dan kwallon yayi karatun ne a Jami’ar Turin ta kasar da ke cikin Birnin da Kungiyar Juventus ta ke.

KU KARANTA: Dino Melaye ya karbi Satifiket din sa a ABU

Wani Dan wasa ya kammala karatun Digirgir
Dan wasa Chiellini ya kammala karatu

Babban dan kwallon ya ba Jama’a mamaki inda ya zama cikin wadanda su ka fi kowa hazaka a aji. Chiellini yayi nazari ne a kan Kungiyar sa ta Juventus inda babban Farfesan nan Pietro Paolo Biancone ne ya duba aikin sa.

An dai ce bikin Danjuma ba ya hana na Magajiya, yanzu haka Juventus na da wasa da Kungiyar Chiveno a wannan mako. Ko a Najeriya dai Shugaban Jami’ar NOUN wanda ake karatu daga gida ya bayyana cewa wannan karo har da wani Fursuna ke shirin shiga karatun digir-digir.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Masu neman shiga Jami'a na shan wahala a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng