Ban aske gashi na ba – Inji Nafisa Abdullahi

Ban aske gashi na ba – Inji Nafisa Abdullahi

Jaruma ‘yar wasan fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta ce bata aske gashin ta ba kamar yadda ake ta yada wa a gari.

Ban aske gashi na ba – Inji Nafisa Abdullahi
Nafisa Abdullahi ta ce bata aske gashinta ba

Nafisa ta saka wata hoton ta ba gashi a kanta a shafin ta na Instagram inda ta yi ma hoton lakabi da 'Na Dawo’.

KU KARANTA KUMA: Sankarau: Mutun 1 ya mutu, yayinda aka kwantar da wani a Kaduna

Ganin yadda hoton ta ke ta yawo a shafunan mutane a yanar gizo da irin nuna rashin jin dadin haka da ga wasu masoyan jarumar, Nafisa ta sanar cewa bata fa aske gashin ta.

Legit.ng ta ruwaito cewa jarumar ta fadi hakan ne a shafin ta na Facebook in da ta ce wannan hoto na wani sabon shirin ta ne.

“Ban aske gashi na ba, gashi na yana nan daram, ga masu yada jita jita wai na aske gashi na Saboda fim.”

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon Baturiyar da ta kawata birnin Lagas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel