Dan tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar na shirin aure
Dan tsohon shugaban kasa Adulsalami Abubakar, Umar na shirin aure sannan kuma hotunan auren sa sun kayatar matuka.
Tsohon shugaban kasa Alhaji Abdulsalami Abubakar ya kasance tsohon janar din soja wanda ya gaji Sani Abacha a matsayin shugaban kasa a mulkin soja na 8.
KU KARANTA KUMA: Ana neman wani Ministan Buhari da karfi da yaji
Legit.ng ta san cewa yana da dalilin yin murna kamar yadda daya daga cikin kyawawan ‘ya’yansa maza Umar Abubakar ke shirin auren masoyiyarsa Hadiza.
Ma’auratan sun saki kyawawan hotunan aurensu kamar yadda zasuyi aure a ranar 15 ga watan Afrilu a garin Minna. Muna taya su murna.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Shin zaka iya auren matar da ta grime ka ko mijin da bai kai ki ba? Kalli wannan bidiyon
Asali: Legit.ng