Yadda wanzami ya illata amarya da sunan kaciya a Kano

Yadda wanzami ya illata amarya da sunan kaciya a Kano

Wani wanzami ya illata wa wata amarya gabanta da sunan cire mata angurya, bayan da mai gidanta ya yi korafi ga mahifinta cewa ta ki ba shi hadin kai.

Yadda wanzami ya illata amarya da sunan kaciya a Kano
Yan sanda sun kama Wanzamin da ya illata amarya da sunan kaciya a Kano

Wannan al'amari dai ya faru ne a wani kauye da ke jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

Legit.ng ta samu labarin cewa mahaifin yarinyar ne da amininsa suka nemi wanzamin domin yi mata magani ta hanyar cire mata anguryar, a inda wanzamin ya yi mata wannan aiki da karfin tsiya, al'amarin da ya janyo aka lahanta mata gabanta.

Yanzu haka dai wannan baiwar Allah ba ta iya yin fitsari ba tare da kwaroron roba ba da likitoci suka sanya mata sannan kuma ana tsammanin sai an yi mata aiki kafin ta koma dai dai.

Tuni dai mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Ali Dangote ya dauki nauyin yi wa yarinyar magani, a inda shi kuma sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya tube wa dagacin garin rawaninsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan'uwan wata mai sana'ar soye-soye da harbin bindiga ya kashe ta sun koka don neman abi masu hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: