Mai shayi ya hallaka dan shekara 12 a jihar Niger bayan aikata luwadi da shi

Mai shayi ya hallaka dan shekara 12 a jihar Niger bayan aikata luwadi da shi

Yan sanda sun sha alwashin kara gurfanar da wani Abubakar, mai siyar da shayi a Ngwayanma, dake yankin Kontagora na jihar Niger, bayan an yanke mashi hukuncin wata daya a gidan yari da kuma cin tarar sa na naira dubu talatin (N30,000) sakamakon yima wani yaro, Aminu mai shekaru 12 fyade.

Mai shayi ya hallaka dan shekara 12 a jihar Niger bayan aikata luwadi da shi
Mai shayi ya hallaka dan shekara 12 a jihar Niger

Wannan hukunci na zuwa ne bayan wanda abun ya afku a kan say a mutu a wani asibiti cikin makon da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: EFCC: Shugaban kasa ba zai sauke Ibrahim Magu ba

An bayyana cewa Abubakar, wanda ake kira da maishayi, ya sace yaron ne daga iyayensa a watan Maris sannan kuma yayi luwadi da shi a kai a kai na tsawon makonni biyu har sai wani makwabcin sa da ya hankalta ya nemi doki.

A lokacin da yan sanda suka zo kama Abubakar, sai suka gano cewa yaron na cikin matsanacin lafiya. A take akayi gaggawan kai shi asibiti inda ya mutu bayan wasu kwanaki.

An yanke ma Abubakar hukuncin ne kafin marigayin ya mutu.

Da yake bayanin al’amarin, wani mazaunin yankin yace:

"Iyayen yaron sun lura da cewan basa ganin yaron don haka suka nemi sanin inda yake daga abokan sa, wanda suka ce basu san inda yake ba. Bayan nan, aka sanar ma yan sanda batun batan nasa. A farkon watan Maris kenan.

"Bayan makonni biyu, wani mutumi ya sanar mana da cewa yaga Aminu tare da Maishayi (Abubakar). Da farko ya karyata cewan yaron na tare da shi. Daga baya aka gano yaron a dakin sa cikin wani mawuyacin hali. Maishayi ya fadi gaskiyan cewa yayi luwadi da shi sau da yawa.

KU KARANTA KUMA: Labari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo

"An kira yan sanda don su kama shi sannan aka kai Aminu asibiti. Amma abun bakin ciki ya rasu a makon da ya gabata. Iyayen bazasu iya cewa komai ba a kan al’amarin a yanzu; domin suna cikin wani irin hali."

Jami’in kula da huldan jama’a na hukumar yan sandan jihar, DSP Elkana James, wanda ya tabbatar da al’amarin ya kara da cewa za’a gurfanar da Abubakar nan bada jimawa ba a matsayin wanda ya aikata kisan kai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin da ya afku a Ile-Ife tsakanin Yarbawa da Hausawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: