Shan zobo na rigakafin cutar hawan jini – Inji Dokta Ochuko

Shan zobo na rigakafin cutar hawan jini – Inji Dokta Ochuko

Binciken ya nuna cewa ganyen zobo ya kunshi sinadarin wadanda ke taimakawa jiki wajen rigakafin cututtukan suga da hawan jini.

Shan zobo na rigakafin cutar hawan jini – Inji Dokta Ochuko
Bincike ya nuna cewa ganyen zobo ya kunshi sinadarin wadanda ke taimakawa jiki wajen rigakafin cututtukan suga da hawan jini

Sakamakon wani bincike da wani kwararre a cibiyar binciken harkokin masana'antu da ke Oshodi jihar Legas, Dokta Ochuko Erukainure ya gudanar a kan ganyen zobo ya tabbatar da cewa ruwan zobo na da matukar tasiri wajen rigakafin hawan jini.

Binciken ya nuna cewa ganyen zobo ya kunshi sinadarin citric acid, Malevich acid da kuma tartaric acid wadanda ke taimakawa jiki wajen rigakafin cututtukan suga da hawan jini.

Da yake karin haske game da binciken, Dokta Ochuko ya ce yana da muhimmanci a rika shan ruwa zobo a duk lokacin da aka kammala cin abinci ba tare da sanya masa sikari ba don ganin ba a gurbata sinadiran da ke cikinsa.

KU KARANTA: Abin da ya sa Naira ta ke shan kashi

Legit.ng ta samu rahoto cewa, Doktan ya ce bin wannan tsari na shan zobo yana taimaka wajen rage kiba, sanyi da kuma wasu cututtuka. Sai dai kuma kwararren ya yi gargadin cewa shan zobo ga mai juna biyu yana da hadari saboda yana iya zubar da cikin .Ya ci gaba da cewa zobon zai iya haifar da zazzabin da jan ido ga mai juna biyu amma ya nuna cewa duk da yake babu wata shaida kan illar shan zobo ga mai shayarwa, amma likitar ya bada shawarar kaurace masa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon binciken farashin kayan lambu

Asali: Legit.ng

Online view pixel