Wata kungiya a jihar Katsina tayiwa mai kosai kyautan N100,000
- Wata kungiyar masu taimako ta taimaka ma wata mai kosai , Amina Abdullahi, yar shekaru 45 da haihuwa
- An bata kudi N100,000 kuma an mika godiya kan taimakon da take yiwa al’umma
Wata kungiyar taimako mai suna, Katsina Forum, ta yi kyauta ga wata mata mai kosai jihar bisa ga kokarin da takewa mutane.
Game da cewar NAN, sun yi mata kyautan kudi N100,000 a taron da suka gudanar a jiya asabar, 1 ga watan Afrili a jihar Katsina.
KU KARANTA: Kungiyar direbobin tanka zasu fara yajin aiki Litinin
Kana kungiyar ta taimakawa wasu mutane 30 da kyaututtuka iri-iri bisa ga ayyukan d sukayiwa mutanen jihar.
Legit.ng ta bada rahoton cewa Alhaji Lawal Buhari, shugaban kungiyar yace wannan taimako da akayi domin karfafa ilimin diya mace ne.
A ranan Talata, 14 ga watan Maris, shugaban SUBEB yace yan mata 8,000 zasu samu kyautan N20,000 domin sayan takardun karatu, kayan makaranta, da sauran abubuwan da zai taimaka musu wajen neman ilimi.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng