Dandalin Kannywood: An kammala wani kayataccen fin din 'Ba Tabbas'

Dandalin Kannywood: An kammala wani kayataccen fin din 'Ba Tabbas'

Daya daga cikin masu shiryawa da kuma daukar nauyin finafinan Hausa, Safwan Kwankwaso, ya bayyana cewar sun yi matukar shan wahala kafin su kammala daukar sabon fim dinsa mai suna Ba Tabbas. A cewarsa, kokarinsu na zuwa da sabon salo a finafinai shi ne babban dalilin da ya sa suka bata lokaci da kudin don ganin kamfaninsa ya zo da irin wannan fim.

Dandalin Kannywood
Dandalin Kannywood

Kwankwaso ya fadi haka ne jim kadan bayan fitar ‘taba ka lashen’ Ba Tabbas a wannan makon. Watau irin dan tsokaci kadan da ake saki kafin fitar tallan fim. Wanda tuni ya fara jan hankalin makallata finafinan Hausa, musamman da yake an ga wani sabon yanayi da fim din yake shirin zuwa da shi.

Legit.ng ta samu labarin cewa Kwankwaso ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a rika shirya finafinai irin wadannan masu cike da ban al’ajabi da rikita dan kallo, domin ‘yar tallar da suka saki, ta sanya mutane tunanin da wace wainar zuka zo.

KU KARANTA: Shin kun san ministan ilimin Buhari?

“Kullum burinmu shi ne zuwa da sabon abu, wanda mutane ba su saba gani ba, domin abin da al’umma suke so kenan, saboda haka fim din Ba Tabbas yana dauke da wani darasi wanda lallai al’umma suna da bukatar samun ilmi a cikinsa.

“Ina son ganin kamfanina na shirya finafinai irin wadannan, wadanda tun kafin su fita za su cika kunnuwan da idanuwan ‘yan kallo, a rika labarinsu a ko’ina har ma a rika tsammaninsu. Wannan ya nuna lallai mutane suna kula da dukkan abin da muke yi.” In ji shi.

Dandalin Kannywood: An kammala wani kayataccen fin din 'Ba Tabbas'
Fitacciyar yar fina finan Hausa Nafisa Abdullahi

Har ila yau ya ce, ganin yadda mutane ke rige-rigen sanya bidiyon Ba Tabbas a kafafen sadarwar zamani, to zai shirya wata gasa ta musamman, wadda za a zakulo zakakuran da suka yi nasara a ba su kyauta mai tsoka.

KU KARANTA: An kama masu kaiwa yan Najeriya hari a India

“Kasancewar mun kashe makudan kudade wajen shirya wannan fim, saboda haka za mu yi masa talla na musamman don ya shiga lungu da sako na garuruwan da ake kallon finafinan Hausa. Shi ya sa za mu shirya gasa ta musamman a soshiyal midiya, tun da yanzu harkokin sun koma can, kuma akwai kyauta ta musamman ga duk wanda ya samu nasarar lashewa.”

Ba Tabbas, fim ne da ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Rahama Sadau, Yakubu Mohammad, Maryam Booth da sauran su. AbdulAziz Dan Small ne ya shirya, yayin da Ali Gumzak ya bada umarni.

Zuwa yanzu dai taba ka lashen fim din ya jefa ayar tambaya a zukatan mutane, shin me ya faru da Rahama Sadau har kamanninta suka sauya kwata-kwata. Domin a dan kadan din tallan, an ganta da kwalkwal, sannan fuskarta ta yi bakikirin kamar wasu kuraje sun fito.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wasu mawakan Najeriya ne ke cashewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel