‘Laifi tudu ne, take naka ka hango na wani’ – Shehu Sani ga Gwamnonin Najeriya

‘Laifi tudu ne, take naka ka hango na wani’ – Shehu Sani ga Gwamnonin Najeriya

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar babu wani gwamnan Najeriya daya isa ya soki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin tabuka komai.

‘Laifi tudu ne, take naka ka hango na wani’ – Shehu Sani ga Gwamnonin Najeriya
Shugaba Buhari

Shehu Sani wani shine ke jagorantar kwamitin kula da basussukan kasa na ciki da waje, ya bayyana haka ne a ranar Talata 28 ga watan Maris bayan kammala taron daya gudana a karamar hukumar Chikun inda ya gana da al’ummomin yankin.

KU KARANTA: Matashi ya datse kan tsohuwa mai shekaru 72 a jihar Ogun

“Na fada na kara, babu wani gwamna daya isa ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin tabuka komai. Ya za’a yi kana amsar kudaden jiha dana kanana hukumomi a duk wata, kuma kace Buhari ya gaza?

“Ba zai yiwu ka amshe kudaden yanayi, kungiyar Paris da na tallafi, kuma kace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza ba,” inji Shehu Sani

Legit.ng ta ruwaito sanatan yana fadin cewa shugaba Buhari ya samu gagarumar nasarori da dama fiye da yawancin gwamnonin Najeriya.

“Idan bakwa so Buhari ya samu amintattu masu fada a ji, kuma ku rushe naku amintattun, idan kuma kuna so Buhari ya saurare ku, toh kuyi aiki. Don haka ina kira ga shugaba Buhari da cewa kada ya sake daga hannun wani dan takara da niyyar a zabe shi, ya kyale jama’a su zabi wanda suke so.

“Ya kamata Buhari ya daina al’adar daga ma yan takarkaru hannu, muna goyon bayansa ya tsaya takara a shekarar 2019, amma ya daina daga hannun yan takarkaru, saboda wadanda yake daga ma hannaye suke kashe Najeriya.” Inji Shenu Sani

Da fari a yayin taron, Sanatan yace yaje ne don jin ra’ayoyin al’ummar yankin dangane da aikin babbar hanya data tashi daga gabashin Kaduna zuwa birnin Abuja. sanatan ya soki lamirin ma’aikatar ayyuka ta tarayya dangane da yadda farashin aikin yayi tashin gwauron zabi zuwa N42b ba tare da tuntuba ba.

“Na zo ne don in saurare koke koken ku dangane da aikin babban hanya na gabashin Kaduna, wanda gwamnatin tarayya ta kara farashinsa zuwa sama da naira biliyan 40. Ina tabbatar muku da cewa gwamnati bata tuntubi wani daga cikin yan majalisun jihar nan ba dangane da hanyar.

“Ina sane da yadda na jajirce kan lallai sai an saka aikin hanyar a cikin kasafin kudi na shekarar 2016-2017, amma kawai sai karantawa nayi wai an kara farashin aikin zuwa N42b. amma ban san yadda ma’aikatar ayyuka na gwamnatin tarayya ta kara kudin haka ba, a gani na ya kamata a ce sun tuntube mu,” inji Shehu Sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon kaddamar da aikin layin dogo daga Legas zuwa Ibadan da Farfesa Osinbajo yayi

Asali: Legit.ng

Online view pixel