Makiya na ne suke cewa na ci mutuncin Buhari - Dan majalisar Bauchi
Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumonin Misau da Damban daga Jihar Bauchi, Hon. Ahmed Yarima ya karyata kuma ya la'anci wadanda suka yi masa kazafin cewa wai ba ya tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Hon. Yarima ya musanta wannan zargin ne a wata tattaunawa da ya yi da majiyar mu a yau da rana a Abuja. Dan Majalisar daga jihar Bauchi ya ce shi bai yi mamaki ba da wasu yara ko 'yan barandan marasa kishin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suka kitsa masa wannan sharrri.
Legit.ng ta tattaro cewa ya kara da cewa hakan ya biyo bayan irin adawar da yake yi ne da gwamnatin jihar Bauchi, saboda gwamnatin ba ta aiki, ta watsar da duk wadanda aka sha wahalar kafa gwamnati da su a jihar.
KU KARANTA: APC da Buhari basu iya mulki ba - Bafarawa
Baya ga wannan, Yerima ya kara da cewa su ne masoya Buhari na ainihi, domin Gwamnan Jihar Bauchi ana saura kwana 40 a yi zabe ya shigo APC.
Ya ci gaba da cewa ya na adawa ne har ila yau da gwamnatin jihar Bauchi saboda ba ta mu'amala da akasarin zababbun 'yan majalisa da sanatocin da ke jihar.
Yerima ya ce kowa ya san irin rashin iya aikin da gwamnan ke yi, yadda a yanzu duk inda ya je, jifar sa ake yi.
KU KARANTA: An kwace motoci 13 a hannun wani sanata
A kan haka, Yerima ya ce, "masu yin sharri su na cewa wai ba mu son Buhari, to Buharin su ke cutarwa. Shi ai ya san mu masoyan sa ne na hakika. Shi kuwa gwamna ai lokacin ya na shugaban Hukumar zabe a jihar Ribas, Buhari kiri'a tara kawai ya samu. Kun ga wai hatta shugabannin jam'iyya duk ba su zabe shi a rahoton INEC.
"Dole mu ke adawa da gwamna, shi ya sa ake yin sharri. Kuma kafin ni, sai da gwamnan ya sa aka nemi a yi wa wani sanata kiranye, amma bai yi nasara ba."
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Bayan dawowar Buhari, kalli sabon bidiyon mu da muka zanta da mutane
Asali: Legit.ng