Jami'ar Ummaru Musa Yar'adua tayi abun azo-a-gani
- A jiya Asabar, 25 ga watan Maris ne Jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Katsina ta yaye dalibai kusan dudu biyar
- Bikin yaye daliban shine karo na biyu da jami'ar ta taba yi
Daliban suna hada da na shekarar 2012/2013; 2013/2014; 2014/2015; 2015/2016, inda ya samu halartar manyan baki ciki har da gwamnoni.
Makarantan ta cika shekara goma da budewa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kammala ayyukan gyara tare da inganta wasu manyan asibitoci guda uku wadanda suka hada da babba asibitin cikin garin Katsina, Daura da na Funtua akan kudi naira biliyan daya da rabi.
KU KARANTA: Bana sa'insa da Saraki - Ndume
Gwamna Aminu Bello Masari ya kuma dauki sabbin ma'aikata da yawansu ya kai 620 daga cikin su akwai kwararrun likitoci 6, sai ma'aikatan jinya da masu karbar haihuwa su 153 sauran jami'an kiwon lafiya daban daban.
Daraktan babban asibitin Katsina Dr. Kabir Mustapha ya bayyana cewa Masari ya kuma samar da gadajen kwantar da marasa lafiya 650 a kowanne asibiti cikin ukun nan tare da kirkirar bangaren awon jikin dan adam da binciken cututtuka.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng