Kimiyya ta gano abin da musulunci ya gano shekaru 1400 da su ka wuce

Kimiyya ta gano abin da musulunci ya gano shekaru 1400 da su ka wuce

Tun fiye da shekaru 1400 da suka wuce a baya Addinin musulunci ya gano amfanin sukari a jikin jinjiri da aka haifa. Sai ga shi yanzu Kimiyya ta san da wannan nazarin

Kimiyya ta gano abin da musulunci ya gano shekaru 1400 da su ka wuce
Kimiyya ta gano abin da musulunci ya gano shekaru 1400 da su ka wuce

Wani ikon Allah, sai bayan shekaru sama da 1400 masana Kimiyya su ka fahimci cewa ashe jinjiri da aka haifa yana bukatar sukari nan take bayan haihuwar sa. Musulmai dai sun dade da sanin wannan tun ba yau ba.

Yana daga cikin Sunnonin Manzon Allah Annabi Muhammad SAW da ya koyar a dauki dabino dan kadan a tauna a sa wa jinjiri a baki da zarar an haife sa. Wannan abu dai shi ake kira Tahniqi da larabci.

KU KARANTA: Ana nema a hana bara a Najeriya

Kimiyya ta gano abin da musulunci ya gano shekaru 1400 da su ka wuce
Kimiyya ta gano amfanin dabino

A wani rahoto da Jaridar BBC tayi ya kuma samu zuwa hannun Legit.ng, Masana kimiyya sun gano cewa yaron da aka haifa yana bukatar sukari kadan da zai hana kwakwalwar sa samun matsala.

A musulunci dai dabino ya zama wani babban abin marmari, wanda da shi ake so mutum ya fara buda baki a lokacin da yayi azumi domin kuwa yana dauke da sinadarai masu kara karfi da kuma matukar amfani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng