Jarumai da dama sun halacin wani taron 'yan fim din Hausa
- Ranar Talatar makon jiya ne kamfanin Apple Integrated Serbicesya jagoranci taron kara juna sani ga masu ruwa da tsaki a harkokin shirya finafina Hausa na Kannywood.
- Taron da aka gudanar a dakin taro na Digital Institute da ke Kano, an shirya ne domin baje kolin basirar masu gudanar da wannan harka, tare da hada gwiwa wajen tattauna hanyoyin inganta harkar finafinan Hausa.
Da yake gabatar da takarda a wurin taron Dakta Ibrahim Ado Kurawa, wanda ya yi tsokaci kan batun al’adu, musamman a harkar shirya finafinan Hausa, ya tabo halin da al’adu suka tsinci kansu a wannan lokaci, sannan kuma ya duba yadda tsara labarai, bada umarni da kuma yadda kwalliya ya kamata ta kasance musamman shigar da ake amfani da ita a lokacin daukar shirin fim din Hausa.
KU KARANTA: Fadan PDP na cikin gida yazo karshe
Saboda haka ya tabbatar da bukatar da ake da ita na inganta al’adunmu tare da lura wajen aron al’ada kamar yadda ake a finafinan Hausa na aro al’adun Indiya ana nunawa Hausawa.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban Kungiyar MOPPAN na jihar Kano Alhaji Kabiru Mai Kaba, Malam Alkanawy, Jarumai, Daraktoci, Marubuta da wakilai daga jihar Jigawa duk suna cikin wadanda suka halarci wannan muhimmin taro na wuni daya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng