Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?

Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?

– Attajiri Bill Gates shi ya fi kowa kudi a Duniya

– Tun shekaru 23 da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya

– Bill Gates ya mallaki sama da Dala Biliyan 86

Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?
Bill Gates ne wanda ya fi kowa kudi a Duniya

Kamar yadda aka saba a wannan shekarar ma dai kasurgumin Attajirin nan ne ya fi kowa kudi a Duniya. Arzikin Bill Gates ma dai karuwa yayi daga Dala Biliyan 75 zuwa Dala Biliyan 86 a bana. Mista Bill Gates shi yake da Kamfanin Microsoft.

Tun shekaru 23 da suka wuce kusan kowace shekara sai ka ga sunan Bill Gates a cikin manyan Attajiran Duniya. Yanzu haka dai shekara hudu kenan a jere babu wanda ya buge Bill Gates a Duniya.

KU KARANTA: Ka ji abin da wani Gwamna yake shirin yi

Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?
Bill Gates da Warren Buffet sun fi kowa kudi a Duniya

A sahun farko na masu kudin Duniya bayan Bill Gate dai akwai irin su Warren Buffet, da kuma Jeff Bezos na Amazon. Sannan akwai Amancia Ortega da Mark Zuckerberg mai shafin Facebook. Akwai sauran Attajirai irin su Carlos Slim Helu na kasar Mexico.

Rahotanni da ke fitowa daga Forbes wannan shekarar sun nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ya fita daga cikin sahun mutane 100 da suka fi kowa kudi a Duniya. A wannan shekarar ne Dangote ya sullubo daga jerin bayan da kuwa yana ciki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel