YANZU YANZU: Janar Buratai na koro ma shugaba Buhari bayani (HOTO)

YANZU YANZU: Janar Buratai na koro ma shugaba Buhari bayani (HOTO)

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai da shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar sun ba shugaban kasa Muhammadu Buhari takaitaccen bayani a kan al’amarin tsaro a kasar.

YANZU YANZU: Janar Buratai na koro ma shugaba Buhari bayani (HOTO)
Buratai ya fada ma yan jaridu cewa yayi amfani da damar tattaunawarsa da shugaban kasa gurin bashi takaitaccen bayani kan ayyukan da sojoji ke ciki

Dukkan shugabannin tsaron guda biyu samu dama don ba shugaba Buhari takaitaccen bayani a kan al’amarin tsaro a cikin ofishin shugaban kasa dake fadar Villa, Abuja a ranar Talata, 21 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Majalisar dattawa ta fara binciken Melaye

Jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasa, Buratai ya fada ma yan jaridu cewa yayi amfani da damar tattaunawarsa da shugaban kasa gurin bashi takaitaccen bayani kan ayyukan da sojoji ke ciki.

A halin yanzu, sakamakon mutuwar mutane 30 a Zaki Biam, karamar hukumar Ukum dake jihar Benue bayan harin da wasu yan bindiga da ake tunanin makiyaya ne suka kai, shugaban kasa Buhari ya nace kan cewa lallai babu wani da ke da ikon daukar rayuwar wani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jihar Benue a sabon harin da aka kai kasuwar Zaki Biam, wanda yayi sanadiyan rasa rayyukan mutane da dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng