Abin da ya sa Hamid Ali ba zai sa rigar kwastam ba

Abin da ya sa Hamid Ali ba zai sa rigar kwastam ba

Wani tsohon Janar na Soja yak are Hamid Ali daga sukar masu suka yace bai ga dalilin da za ace Kanal Hamid Ali mai ritaya ya sa kakin kwastam ba

Abin da ya sa Hamid Ali ba zai sa rigar kwastam ba
Abin da ya sa Hamid Ali ba zai sa rigar kwastam ba

Makon jiya Sanatocin Najeriya su ka gayyaci shugaban kwastam na kasa watau Hamid Ali zuwa Majalisar inda kuma ta kora sa bayan ya zo ba tare da ya sa kayan hukumar ba. Yanzu haka Majalisar ta nemi Hamid Ali ya dawo wannan makon tare da rigar sa ta Hukumar.

Wani tsohon Gwamna a lokacin mulkin Soji Manjor Janar David Jemibewon yace bai ga dalilin da za a ce sai Hamid Ali ya sa rigar kwastam ba alhali ba Ma’aikacin hukumar bane. Hamid Ali dai tsohon Kanal din Soja ne da aka nada domin ya shugabanci hukumar ta kasa.

KU KARANTA: Buhari aiki yake yi har a gida

CG Customs Hamid Ali
Hamid Ali ba zai sa rigar kwastam ba

Manjo Janar din mai ritaya yace Majalisar Dattawa ce kurum ta ke kirkiro rikici ana zaman lafiya. Janar din yace ai cin mutunci ne ma a ga tsohon Soja iya Soja irin Hamdi Ali a cikin kayan Hukumar fasa kauri na kasa.

Kwanaki muka samu labara cewa ita ma Majalisar wakilai na shirin binciken Hamid Ali mai ritaya game da kayan da hukumar ta karbe ta kuma ki fitar da su. Majalisar tace ya kamata hukumar kwastam ta fitar da kayan da ta kama domin Jama’a su saya a farashin da ya dace.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel