Jihohin Kano da Katsina ne na daya da na biyu wajen yawan 'yan kwaya a Najeriya - Rahoto

Jihohin Kano da Katsina ne na daya da na biyu wajen yawan 'yan kwaya a Najeriya - Rahoto

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama mutum 34,499 kan laifukan da suka danganci tu'ammali da miyagun kwayoyi a jihohi 36 da kuma babban birnin kasar daga tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015.

Jihohin Kano da Katsina ne na daya da na biyu wajen yawan 'yan kwaya a Najeriya - Rahoto
Jihohin Kano da Katsina ne na daya da na biyu wajen yawan 'yan kwaya a Najeriya - Rahoto

A wani rahoto da ta fitar, NDLEA ta ce jihar Kano da ke Arewa maso Yamamcin kasar ce kan gaba wajen yawan masu amfani da kwayoyin da ke sa maye, sai jihar Katsina ta biyu, sai jihar Filato ta uku da kuma jihar Ekiti ta hudu.

Kwamandan hukumar ta reshen jihar Kano, Hamza Umar, ya shaida wa majiyar mu cewa mafi yawan mutanen da aka kama da laifin, masu shan kananan kayan maye ne irin su Tramol da magungunan tari da ake sha ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: Darajar Naira zata kara yin sama - CBN

Ya kuma ce jihar Kano ta zama kan gaba ne saboda ita ce ta fi ko wacce jiha yawan al'umma.

Haka kuma shiyyar Arewa maso Yamman ce aka fi samun laifukan fiye da sauran shiyyoyin kasar biyar, inda aka samu masu laifin ta'ammali da kwayoyin har 8,939.

Shiyyar Kudu maso Yamma ce ta biyu da laifuka 6,999, sai shiyyar Arewa ta tsakiya da laifuka 5,574.

Ta hudu ita ce shiyyar Kudu maso Kudancin kasar inda aka samu laifuka 5,545.

Shiyyar Kudu maso Gabashin kasar ce ta biyar da laifuka 4,230 sai kuma shiyyar Arewa maso Gabas da laifuka 3,212.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: