Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya kafa kwamitin mai da jirgin sama (HOTUNA)
Wani babban dan jarida mai suna Ahmad Manage Bauchi ya rubuta cewa Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya kafa kwamitin da dai mai da jirgin saman Bauchi zuwa safara wanda data rinka kawo ma jihar Bauchi kudin shiga.
Gwamna Abubakar ya kira ga yan kwamitin da su tambatar da cewa wannan jirgin Bauchi tana aiki kuma aikin ta dai shafi jihar Bauchi ne domin bunkasa tattalin arzikin kasa musamman yawon shakatawa da sauran su.
KU KARANTA KUMA: Nan da wata uku za'a fara fitar da man fetur a jihar Bauchi
Yan kwamitin sun hada da Air Commodore AT Baba Gamawa, babban mai bawa gwamna shawara da kwamishinan gidaje da ayyuka na jihar Bauchi AT Ali da kuma daraktan bunkasa tattalin arzikin jiha Aminu Musa.
Yan kwamitin sun ziyarci kanda yanzu haka wannan jirgin saman Bauchi take a hannun kamfanin safara nan na OverLand, ana sa ran yan kwamitin da su mika rahoton sune dama bada shawaran ta yaya za'a yi anfani da wannan jirgin saman Bauchi domin kawo kudin shiga ma jihar Bauchi.
Ku kalli hotuna a kasa:
Ku kasance tare da mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/
Da anan https://twitter.com/naijcomhausa
Ku kalli bidiyon kan gyaran jirgin kasa a Najeriya
Asali: Legit.ng