INALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJIHUN: Sarkin Pawan Katsina ya rasu da shekaru 103

INALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJIHUN: Sarkin Pawan Katsina ya rasu da shekaru 103

Allah ya wa Alhaji Muhammadu Lawal-Areda, hakimin karamar hukumar kankara a jihar Katsina rasuwa.

INALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJIHUN: Sarkin Pawan Katsina ya rasu da shekaru 103
INALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJIHUN: Sarkin Pawan Katsina ya rasu da shekaru 103

Allah ya wa Alhaji Muhammadu Lawal-Areda, hakimin karamar hukumar kankara a jihar Katsina rasuwa. Hakimin ya rasu ya na da shekaru 103 a duniya.

Iyalan marigayin suka tabbatar da mutuwar basarakan ga kamfanin dilancin labarai na Najeriya (NAN) a Kankara a ranar Juma'a, 17 ga watan Maris.

Majiyar ta ce an binne margayin bayan sallar juma’a a Kankara.

Cikin wadanda suka halarci jana'izar sun hada da sarakunan jihar Katsina, Alhaji Abdulmunin Kabir da sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, da kuma sauran sarakunan jihar.

Sun hada kuma da Ambasada Tukur Mani, tsohon shugaban babban kotun tarayya, Justice Adamu Bello. Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari da kuma mukaddashin shugaban karamar hukumar Kankara, Alhaji Bishir Maikano.

Marigayin ya bar mata 3, yara 34 da kuma jikoki da dama.

Wasu daga cikin 'ya'yansa sun hada da tsohon shugaban karamar hukumar Kankara, Alhaji Abubakar Lawal da mai ungwar Zango-Zabaro, Alhaji Abdullahi Namashi, da kuma Alhaji Tanimu Lawal, da sauransu.

NAN ta ruwaito cewa an nada saraki Lawal-Areda a watan Fabrairu 2, 1972.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng