An karawa Ma’aikatan N-Power albashi

An karawa Ma’aikatan N-Power albashi

- Shugaba Buhari ya karawa Ma’aikatan N-Power albashi

- Shugaban kasar ya amince da karin N4500 ga kowane Ma’aikaci

- Wannan kari dai na sayen na’urar aiki ne

An karawa Ma’aikatan N-Power albashi
An karawa Ma’aikatan N-Power albashi

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi abin da zai sa Ma’aikatan N-Power murmushi inda ta amice da karin N4500 a albashin kowane Ma’aikaci. An kara wannan kudi ne saboda Ma’aikatan su samu daman sayen na’urar da za ta taimaka wasu wajen aiki.

Idan dai ba a manta ba Gwamnatin Buhari ta dauki matasa har 20, 000 aiki inda ake horas da su kuma ake biyan su N30, 000 a kowane wata. Yanzu haka dai an kara masu albashi saboda su saye na’urar da za ta rika taimaka masu wajen aiki.

KU KARANTA: 'Yan fashi sun sallama a Zamfara

Mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasa watau Laolu Akande ya bayyana haka. Yace za a rika cirewa Ma’aikatan kudi a albashin su har na watanni 20 domin su mallaki irin na’urar da suke so wajen aiki.

Haka kuma dai jiya ne shugaban Majalisar dattawa Dr. Abubukar Bukola Saraki ya bayyana cewa Majalisa ta kusa gama aiki game da kasafin kudin wannan shekarar. Saraki ya bayyana haka ne bayan sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng