Dan wasa Xabi Alonso zai ajiye kwallo

Dan wasa Xabi Alonso zai ajiye kwallo

– Babban dan wasa Xabi Alonso zai yi ritaya

– Dan wasan na tsakiya ya yace daga kakar bana shikenan

– Alonso ya bugawa Liverpool da Real Madrid kwallo

Dan wasa Xabi Alonso zai ajiye kwallo
Dan wasa Xabi Alonso zai ajiye kwallo

Babban dan wasan tsakiyar nan na kasar Spain Xabier Alonso Olano yace zai ajiye tamula a karshen wannan shekarar. Xabi Alonso ya bayyana wannan matakin da ya dauka ne kwanan nan, yace ba don yana so ba.

Alonso yace ya yanke wannan shawarar ne bayan yayi nazari. Xabi dai yana takawa kungiyar Bayern Munchen leda ne a yanzu haka. Xabi dan wasan tsakiya ne kwararre kuma mutum maras hayaniya a fili da waje.

KU KARANTA: Ka ji abin da aka yi wa wani Sanata?

Xabi Alonso ya fara kwallon sa ne a gida Real Socieded da ke kasar Spain, sannan ya wuce Liverpool inda ya ci kofin ‘Champions League’ daga nan ya komo Real Madrid inda ya kara samun nasarar lashe wannan kofi. Xabi zai ajiye wasa yana da shekara 35 yace tun kafin abin ya gagare sa.

A kasa kuma, Mai kula da ‘Yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya mikawa Ahmed Musa kambun Super Eagles a dalili da cewa kyaftin din kungiyar John Mikel Obi ba zai buga wasannin da za a kara masu zuwa nan gaba ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel