Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

Tushen zamantakewar aure na mallam Bahaushe ta kan fara ne daga lokacin da saurayi ko bazawari ko miji yace yana son budurwa, bazawara ko mata.

Daga sanda alaƙar soyayya ta ƙullu a tsakaninsu, to fa zamantakewar aure ta fara shiga, domin kuwa irin tarbiyya da atisayen da suka bai wa kansu a wannan lokacin, ita za ta girmama ko ta bunƙasa a lokacin da suka yi aure. Idan suka bawa kansu atisaye mai kyau, to wannan na nuna cewa za’a samu zamantakewar aure mai kyau.

Bisa al’ada akwai irin zaman auratayyar da Malam Bahaushe ya saba da shi, to amma zuwan wannnan zamanin da muke ciki ya kawo sauye-sauye da dama, tun daga kan neman auren shi kansa har zuwa zaman auren. Bugu da ƙari, bambancin ra’ayi da ilimin zamani sun taka muhimmiyar rawa wajen canza zamantakewar auren Malam Bahaushe da ma zamantakewarsa ta yau da kullum baki ɗaya.

KU KARANTA KUMA: Fada ya barke yayinda wani mutumi ya sanya wa Karen sa suna Muhammad a Kaduna

Wannan ita ta kawo yanzu akwai zamantakewar aure iri daban-daban a ƙasar Hausa, irin zaman da wannan yake yi da matarsa daban da irin zaman da wancan ya ke yi da tasa matar saɓanin zamanin baya da za ka ga kusan duk zaman iri ɗaya ne sai ɗan abin da ba a rasa ba.

Ga hotunan yanayin dakin Amaren Mallam Bahaushe a shekarun baya:

1. Kayan gado da Akushi

Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

2. Jeren samiru a saman kwaba

Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

3. Kayan lefe wanda sai yar gata ke samun haka a lokutan baya

Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

4. Manyan langa wanda akanyi amfani dasu gurin kai abinci musamman lokacin bikukuwa

Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

5. Dakin Amarya yar gata a lokutan baya

Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya

Tabbass al'adan mallam Bahaushe ta kasance mai ban sha'awa a wannan lokaci, sannan babu sagwama domin har talaka ma na samun rufin asirin yiwa 'ya'yansa kayan daki ba tare da fargaba ko jiyayi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel