Yau ake bikin ranar mata ta duniya, ku kalli abinda ya faru a Najeriya (HOTUNA)
- Majalisar dinkin duniya ta kebe kowacce ranar takwas ga watan Maris a matsayin ranar tunawa da mata domin nuna mutuntawa da godiya da kuma kauna ga matan saboda gudunmuwar da suke bayarwa ga ci gaban al'umominsu ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da ma siyasa
- A Najeriya kuma musamman jihar Legas, wasu mata sun gudanar da zanga-zangar a gidan gwamnan Legas kan bikin ranar mata ta duniya
Taken bikin na bana dai shi ne 'Ki nuna karfin hali wajen kawo sauyi a rayuwarki'.
To sai dai alamu na nuna ire-iren wadannan bukukuwan ba su da tasiri ga rayuwar matan da ke zaune a yankunan kankara, domin kuwa mafi akasarinsu ma basu san da wannan rana ba.
Mata dai na fuskantar kalubale da dama a rayuwarsu, kama daga cin zarafi zuwa wariya da ake nuna musu musamman a kasashe masu tasowa.
A kan hakane aka kebe wannan rana domin wayar da kan matan sanin 'yancinsu, da kuma nuna musu cewa suma za a iya damawa da su a fannoni da dama na rayuwa.
A shekarar 1975 ne aka fara gudanar da bikin wannan rana.
Ga karin hotuna a kasa
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng