Gwamnan jihar Kaduna ya haramta bara, talla, da aikin achaba
Gwamnatin jihar Kaduna krkashin jagirancin Nasir El-Rufai ta haramta talla, bara da kuma aikin achaba a jihar Kaduna da kewaye.
Wannan labara na fitowa ne bayan majalisar tsaron jihar ta gana a jiya Talata, 8 ga watan Maris a gidan gwamnatin jihar.
Bayan Magana da manema labarai, mai Magana da yawun gwamna ElRufai, Samuel Aruwa, yace an yanke wannan shawara ne domin tabbatar da tsaro bisa ga labaran da ka samu na yunkurin tada tarzoma a jihar.
KU KARANTA: Shin meyasa yan Shi'a basu son birnin Makkah?
Yayi bayanin cewa dokar zata fara aiki yanzu har ranan da Allah yayi.
Yace: “Majalisar tsaro jihar Kaduna ta alanta haramcin bara, talla da kuma amfani da Babura wato achaba a birnin jihar Kaduna da kewaye.
“Rahotannin nda jami’an tsaro suka samu ne ya wajabta wannan doka. Kana kuma an umurcesu da su tabbatar da cewa babu wanda ya saba wannan dokan hana bara, talla da aikin babur.
“Saboda haka ana kira ga mutanen jihar su hada kai da jami’an tsaro yayin tabbatar da wannan doka. Babu babur din da za’a yarda ya dauki wani fasinja.”
Wannan abu na faruwa ne bayan an alanta cewa za’a kulle babban filin jirgin saman Abuja kuma ayi amfani da na Kaduna a madadinshi.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng