‘Nono’ ya tsiro a kirgin wani mutumi bayan ya rusa alkawarin aure da yayi ma wata budurwa (HOTUNA)
Hotunan wani mutumi yayi yawo a yanar gizo sannan kuma ya ja hankulan mutane da dama, kamar yadda aka hango shi a wani sashin addu’a na coci.
A cewar hoton wanda aka buga a shafin sadarwa na Facebook na Brian Jonah Dennis, ya rahoto cewa nono ya fara tsirowa a kirgin wannan mutumin bayan budurwarsa tayi mai asiri.
KU KARANTA KUMA: Ana siyar da buhun shinkafa kan N8,000 a Lagas (kalli HOTUNA)
Ya ce: “Wannan mutumin yayi alkawarin auren wata yarinya amma ya ki cika alkawarin don haka tayi mai asiri kuma a yanzu yana dauke da nono a kirjin sa. Dan Allah idan na taba yi maki alkawarin aure, turo mun adireshin kauyen ku don na zo nag a mutanen ki, bana so na kare kamar wannan.”
Kalli rubutun a kasa:
Wannan abun dariya ne!
Asali: Legit.ng