Dalilai 7 da ke sa fastoci zuwa wurin bokaye don yin tsafi

Dalilai 7 da ke sa fastoci zuwa wurin bokaye don yin tsafi

-Ba sabon labari ba ne irin yadda wasu malama Coci-coci ke yin tabargaza da sunan addini sai dai yawan tsafe-tsafe na yawaita da sunan baiwa ko dauakak daga Ubangiji

-Mun ji labarai na fastoci da su ke amfani da gurbatattun hanyoyi don samun nasara a harkokinsu na coci, ga wasu dalilai 7 da ake zargin su ke ingiza fastoci ke zuwa wurin bokaye don yin tsafi

Dalilai 7 da ke sa fastoci zuwa wurin bokaye don yin tsafi
Wasu fastoci a yayin gudanar da ibada a cocinsu

A wani lokaci da ya wuce an zargi wani fasto Stephen Maduabuchi da kokarin binne wani asiri don bunkasar cocinsa.

A bara an kama wani fasto na Cocin Christ Apostolic Church, Moses Abiodun bisa binne wani abu da ake zargin kan mutum ne a Cocinsa.

Da wasu mutanen da dama da aka kama da irin wadannan laifuffuka. Abin bakin ciki ne a ce coci na cike da yaudara.

Mu na zaune a duniyar da ke cike da yaudara da karya. Fastoci su na so su burge mambobinsu da ke masu kyakkyawan zato.

'Yan Najeriya su na son samun sauki cikin gaggawa, shi ya sa fastoci ka iya yin komai don samun dama ko da kuwa hanyar shedan ce don su burge jama'a. Za ku yi mamaki ta ya ya wadannan mutane su ke amfani da tsafi. Ga dalilan:

1. Don samun yawan mambobi

Iya yawan mambobi iya yawan kudin da za a samu. Kuma in sun samu kudi da yawa, za su samu damar rayuwa mai kyau. Wasu fastocin za su iya yin komai don su ja hankalin mutane ko da kowa za su bautawa shedan.

2. Don samun kudi

Matsakaiciyar coci a Najeriya na gudanar da ibada a kalla sau hudu duk Lahadi kuma ana karbar sadaka a kowane lokaci. Kai, za ma ka iya bada sadakar ta yanar gizo a yau. Wasu fastocin sun fi son kudi fiye da goyon bayan jama'a. Alkawarin kudi ya zama ginshikin yawancin hudubobin da ake yi. Wadannan fastoci sun san yadda za su yi amfani da huduba su sa mutane su bada kudi.

3. Don neman shuhura

Yanzu wasu fastocin sun fi son shuhura maimakon aikin ubangiji . Ba su san yadda za su bambance tsakanin ci gaban shi mai wa'azi da na Linjila ba. Kawai sun fi so su hau manyan motoci, su dinga zaga duniya ba tare da sun kula ko magoya bayansu na jin yunwa ba.

Dalilai 7 da ke sa fastoci zuwa wurin bokaye don yin tsafi
Wasu fastoci na kokarin nuna karama don birge jama'a

4. Don nuna karamomi

Idon 'yan Najeriya a rufe ya ke game da karama, har ta kai ba sa iya gane abin da ba dai-dai ba. Da yawa daga mutane na zuwa coci saboda karama, shi ya za ka ga dubunnan mutane na cinicirindo a ire-iren wadannan cocina da ake nuna karama, kai har da tayar da matacce.

Tunda 'yan Najeriya su na son addini kuma sun yi imani da karama sosai, fastoci suna amfani da ita wajen samun makudan kudade.

Wasu 'yan Najeriya sun zama rakumi da akala. Ya wani zai ce ka biya miliyoyi saboda karama, ba ka karanta Linjilarka ne? Ka taba ganin wajen da Yesu ya tambayi kudi kafin ya warkar da wani?

5. Don tabbatar da zaton da ake masu

Mutane da yawa sun kasa gane cewa fastoci ma fa mutane ne. Su na zaton za su magance masu duk matsalolinsu, su warkar da duk wata cuta sannan su sauko masu kudi daga sama. Bisa wannan dalili ne, wasu fastocin ke amfani da gurbatacciyar hanya don tabbatar da zaton da magoya bayansu ke masu.

6. Don jan ragamar jama'a

Ka san mulki da dadi. Wasu fastocin kan zabi tsafi don su ja ragamar jama'a, su dinga bin umarninsu. Wasu ma sun zama bayin fastocinsu. Duk abinda su ka sa su sai sun yi.

7. Jin dadin mayar da su ababan bauta

Su na so a dinga bauta masu. A dinga ganinsu kamar ubangiji, mutane su dinga dogara da su kan komai.

Ga wani ra'ayin jama'a kan lafiyar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel