Na kama mata ta da tsohon mijinta a kan gado na karara

Na kama mata ta da tsohon mijinta a kan gado na karara

- Wani magidanci mai suna Gbenga Akinade ya sanar da kotu cewa ya kama matarsa akan gadonsu na aure tare da tsohon mijinta suna aikata lalata karara

- Gbenga ya roki kotu da ta warware wannan aure nasu

- Ya ce dalilin haka ba zai iya ci gaba da zama da ita ba

Na kama mata ta da tsohon mijinta a kan gado na karara
Na kama mata ta da tsohon mijinta a kan gado na karara

Ya ce ko a lokacin da ya aure ta bai san cewa ita bazawara ba ce kuma ta na da ‘ya’ya biyu duk ya dauka budurwa ce.

Gbenga yace a lokacin da suka hadu ta na sana’ar siyar da maganin garjiya wanda ake kira Agbo-jegi da yarban ci.

Ya kuma ce ya fara ganewa ta na aikata irin wannan aiki ne bayan haihuwar ta na biyu da shi.

“Busayo ta kan bar gida har na tsawo kwanaki biyu zuwa uku inda ta kan kai ‘ya’yan mu makwabta.”

KU KARANTA: Tsagerun Neja delta sun dauki mataki

Akinade yace a ranar da ya kama ta da tsohon mijin na ta suna lalata ya yi ma ta dan karan duka amma yace bai daki tsohon mijin ba domin ya san idan hakan ya faru abin zai yi muni.

Ya roki kotu da ta warware aurensu kuma ta bashi ikon rike ‘ya’yan da suka haifa tare sannan ya dauki alkawarin basu kulan da ya kamata.

Busayo ta fada wa kotun cewa Akinade ya san cewa ita ba bazawara ba ce kuma har da ‘ya’yanta biyu amma bata musanta zargin da mijinta ya yi ma ta ba akan aikata lalata da tsohon mijinta da tayi.

Ta roki kotun da ta warware aurensu domin kullum mijin na ta lakada mata duka yake yi.

Ta ce a shirye take domin ta bar gidan mijin na ta sannan yarda ta bar mishi ‘ya’yan na su kama yadda ya bukata.

Alkalin kotun Mukaila Balogun ya warware auren domin basa son junan su bayan sauraren kowanen su.

Balogun ya yanke hukuncin cewa ‘ya’yan su biyu su zauna da mijin, dan su na uku kuwa zai zauwan da matar sanan mijin zai ringa biyan ta 4,000 kowane wata domin kula da yaron.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng